18
Hezekiya sarkin Yahuda
(2 Tarihi 29.1,2; 31.1)
1 A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki. 2 Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya* Da Ibraniyanci Abi, wani sunan Abiya. ’yar Zakariya. 3 Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi. 4 Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)
5 Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa. 6 Ya manne wa Ubangiji, bai fasa binsa ba; ya yi biyayya da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa. 7 Ubangiji kuma ya kasance tare da shi, ya yi nasara a duk abin da ya sa hannu. Ya yi tawaye ga sarkin Assuriya, ya ƙi yă bauta masa. 8 Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.
9 A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta. 10 A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila. 11 Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes. 12 Wannan ya faru ne domin ba su yi biyayya ga Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsu; da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su saurari umarnin ba, balle su kiyaye su.
(2 Tarihi 32.1-19; Ishaya 36.1-22)
13 A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su. 14 Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda. 15 Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.
16 A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.
Sennakerib ya yi wa Urushalima barazana
17 Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki. 18 Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.
19 Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya,
“ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama? 20 Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye? 21 Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi. 22 Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?
23 “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu! 24 Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai? 25 Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”
26 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”
27 Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”
28 Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya! 29 Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba. 30 Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’
31 “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa, 32 har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu!
“Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ 33 Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya? 34 Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna? 35 Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
36 Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.”
37 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.