5
Ananiyas da Saffiratu
1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. 2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.
3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? 4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”
5 Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru. 6 Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.
7 Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba. 8 Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?”
Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”
9 Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”
10 Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta. 11 Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan.
Manzanni sun warkar da mutane da yawa
12 Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon. 13 Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai. 14 Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa. 15 A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa. 16 Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
An tsananta wa manzanni
17 Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. 18 Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa. 19 Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. 20 Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
21 Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane.
Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. 22 Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce, 23 “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.” 24 Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.
25 Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.” 26 Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.
27 Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. 28 Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”
29 Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane! 30 Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace. 31 Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila. 32 Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”
33 Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su. 34 Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci. 35 Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan. 36 Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje. 37 Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su. 38 Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe. 39 Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”
40 Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.
41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. 42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.