12
Bikin Ƙetarewa
Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna a Masar, “Wannan wata za tă zama a gare ku wata na farko, wata na fari na shekararku. Ka faɗa wa dukan jama’ar Isra’ila cewa a rana ta goma ga wannan wata, kowane mutum zai ɗauki ɗan rago domin iyalinsa, ɗaya domin kowane gida. In akwai wani gidan da ba za su iya cinye rago guda ɗungum ba, saboda iyalin kima ne, to, sai su haɗa kai da maƙwabtansu, su ɗauki rago guda gwargwadon yawansu, bisa ga abin da mutum guda zai ci. Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki. Za ku turke dabbar har rana ta goma sha huɗu ga wata, wato, sa’ad da dukan taron jama’ar Isra’ila za su yanka ragunansu da yamma. Sa’an nan za su ɗauki jinin, su shafa a gefen da yake saman dogaran ƙofa na gidajen da suke cin naman dabbobin. A wannan dare, za su gasa naman, su ci da ganyaye masu ɗaci, da kuma burodi marar yisti. Kada ku ci nama ɗanye, ko kuma dafaffe, amma a gasa shi, da kan, da ƙafafun, da kuma kayan cikin. 10 Kada ku bar kome yă kai gobe, abin da ya kai gobe kuwa, sai ku ƙone shi. 11 Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji.
12 “A wannan dare, zan ratsa Masar, in bugi kowane ɗan fari, na mutum da na dabba, zan kuma hukunta dukan gumakan Masar. Ni ne Ubangiji. 13 Jinin zai zama alama a gare ku, a gidajen da kuke; sa’ad da kuwa na ga jinin, zan ƙetare ku. Ba wata annoba mai hallakarwa da za tă taɓa ku yayinda na bugi Masar.
14 “Wannan rana za tă zama muku abin tunawa dukan zamananku masu zuwa, za ku kiyaye ta kamar biki ga Ubangiji, dawwammamiyar farilla ce har abada. 15 Kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti. A rana ta fari, za ku fid da yisti daga gidajenku gama duk wanda ya ci abu mai yisti daga rana ta fari har zuwa rana ta bakwai, za a fid da shi daga Isra’ila. 16 A rana ta fari, za ku yi taro mai tsarki, haka kuma za ku sāke yi a rana ta bakwai. Kada ku yi aiki a waɗannan ranaku, sai dai ku shirya abinci domin kowa, abin da za ku yi ke nan kawai.
17 “Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti domin a wannan rana ce na fitar da ku ɓangare-ɓangare daga Masar. Ku kiyaye wannan rana ta zama muku dawwammamiyar farilla wa tsara masu zuwa. 18 A wata na fari, za ku ci burodi marar yisti daga yammancin ranar goma sha huɗu har zuwa yammancin ranar ashirin da ɗaya. 19 Kada a sami yisti a gidajenku har kwana bakwai. Kuma duk wanda ya ci wani abu mai yisti, za a fid da shi daga taron jama’ar Isra’ila, ko baƙo ne, ko haifaffen ɗan ƙasa. 20 Kada ku ci wani abincin da aka yi da yisti. Ko’ina kuka zauna, dole ku ci burodi marar yisti.”
21 Sa’an nan Musa ya kira dukan dattawan Isra’ila ya ce musu, “Ku je da sauri ku zaɓi dabbobin iyalanku, ku yanka ragon Bikin Ƙetarewa. 22 Ku ɗauki ƙunshin itacen hizzob, ku tsoma cikin jinin da yake a kwano, ku yayyafa wa dogaran ƙofa duka biyu, da bisa kan ƙofar. Kada wani daga cikinku yă fita daga ƙofar gidansa sai da safe. 23 Sa’ad da Ubangiji yake ratsa ƙasar don yă bugi Masarawa, zai ga jinin a bisa da kuma gefen madogaran ƙofa, zai ƙetare ƙofar, ba zai bar mai hallakawa yă shiga gidajenku, yă buge ku ba.
24 “Ku kiyaye waɗannan dokokin a matsayin dawwammamiyar farilla, da ku da ’ya’yanku har abada. 25 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki. 26 Sa’ad da kuma ’ya’yanku suka tambaye ku, ‘Mece ce manufar wannan biki?’ 27 Sai ku faɗa musu, ‘Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ ” Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada. 28 Isra’ilawa suka tafi suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna.
29 Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi. 30 Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.
Fitowa
31 A cikin daren, Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna ya ce, “Ku tashi, ku da jama’arku, ku fita daga cikin jama’ata. Ku tafi, ku bauta wa Ubangiji yadda kuka ce. 32 Ku kwashi garkunanku na tumaki da na awaki, da na shanu, ku yi tafiyarku kamar yadda kuka ce, amma ku sa mini albarka.”
33 Masarawa suka matsa wa Isra’ilawa su fita daga ƙasarsu da sauri. Gama mutanen Masar sun ce, “Ai, za mu mutu duka, in ba su tafi ba!” 34 Sai mutanen suka ɗauki garin da sun kwaɓa ba yisti a ciki, tare da ƙwaryansu na aikin kwaɓan, suka nannaɗe su a mayafansu, suka rataye a kafaɗunsu. 35 Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Musa ya umarce su, suka roƙi Masarawa kayan adonsu na azurfa da na zinariya, da kuma tufafi. 36  Ubangiji kuwa ya sa Isra’ilawa suka yi farin jini a wurin Masarawa, Masarawa kuma suka saki hannu wa mutanen, suka ba su duk abin da suka roƙa; ta haka Isra’ilawa suka washe Masarawa.
37 Isra’ilawa suka kama tafiya daga Rameses zuwa Sukkot. Akwai maza dubu ɗari shida da suke tafiya da ƙafa, ban da mata da yara. 38 Waɗansu mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba, suka haura tare da su, da garkunan shanu, da na tumaki da awaki. 39 Suka toya burodi marar yisti da garin da aka kwaɓa wanda suka kawo daga Masar. Garin da aka kwaɓan ba shi da yisti, domin an kore su daga Masar, ba su kuwa sami damar shirya wa kansu abinci ba.
40 Zaman da Isra’ilawa suka yi a Masar, ya kai shekara 430. 41 A ranar da shekara 430 ɗin nan suka cika, a ran nan ne dukan ɓangare-ɓangare na mutanen Ubangiji suka bar Masar. 42 Gama Ubangiji ya yi tsaro a wannan dare, domin yă fitar da su daga Masar, a wannan dare, dole dukan Isra’ilawa su yi tsaro, don su girmama Ubangiji, cikin dukan tsararraki masu zuwa.
Abubuwan da Bikin Ƙetarewa ya hana
43  Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Waɗannan ne ƙa’idodin Bikin Ƙetarewa.
“Ba baƙon da zai ci shi. 44 Duk bawan da kuka sayo, yana iya ci, in dai an yi masa kaciya, 45 amma wanda ba ya zama tare da ku na ɗinɗinɗin, da kuma wanda aka ɗauki hayansa, ba zai ci ba.
46 “Dole a ci shi a cikin gida ɗaya; kada a kai naman waje. Kada a karya wani daga ƙasusuwansa. 47 Dole dukan taron jama’ar Isra’ila su yi bikin.
48 “Baƙon da yake zama tare da ku da yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi wa dukan mazan da suke cikin gidansa kaciya; sa’an nan ne zai iya yin abubuwa kamar haifaffen ɗan ƙasa. 49 Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta shafi ɗan ƙasa da kuma baƙon da yake zama a tsakaninku.”
50 Dukan Isra’ilawa suka yi na’am da shi, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa da Haruna. 51 A wannan rana, Ubangiji ya fito da Isra’ilawa ɓangare-ɓangare daga Masar.