24
1 “Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba?
Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan?
2 Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su;
suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.
3 Suna ƙwace wa marayu jakunansu
suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.
4 Suna ture matalauta daga hanya
suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.
5 Kamar jakunan jeji a hamada,
matalauta suna aikin neman abinci
gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.
6 Suna girbi a gonakin da ba nasu ba,
suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.
7 Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara;
ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.
8 Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu,
sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.
9 Ana ƙwace jinjiri mai shan mama;
ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.
10 Don ba su da tufafi suna yawo tsirara;
suna dakon dammunan hatsi
amma duk da haka suna cikin shan yunwa.
11 Suna matse zaitun a cikin kunyoyi
suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.
12 Ana jin nishin masu mutuwa daga birni,
kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako.
Amma bai ba wani laifi ba.
13 “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye,
waɗanda ba su san hanyoyinsa ba
ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba.
14 Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi;
yă je yă kashe matalauta da masu bukata;
a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo.
15 Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai;
yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’
sai kuma yă ɓoye fuskarsa.
16 Cikin duhu mutane suna fasa gidaje,
amma da rana sukan kulle kansu;
ba sa so wani abu yă haɗa su da haske.
17 Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu;
suna abokantaka da razanar duhu.
18 “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa;
gefen ƙasar da suke, an la’anta ta,
yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu.
19 Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke,
haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi.
20 Waɗanda suka haife su za su manta da su,
tsutsotsi za su cinye su;
ba za a sāke tunawa da mugaye ba
amma an sare su kamar itace.
21 Suna cutar macen da ba ta da ɗa,
suna nuna wa gwauruwa rashin alheri.
22 Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi,
ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa.
23 Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali,
amma idanunsa suna kansu.
24 Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci,
amma kuma za su ɓace; za su fāɗi
a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi.
25 “In wannan ba haka ba ne,
wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?”