6
Gargaɗi a kan wawanci
Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,
in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
in maganarka ta taɓa kama ka,
ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;
da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka,
ka tafi ka ƙasƙantar da kanka;
ka roƙi maƙwabcinka!
Ka hana kanka barci,
ko gyangyaɗi a idanunka ma.
Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,
kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
 
Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
Ba shi da jagora
ba shugaba ko mai mulki,
duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
 
Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
Yaushe za ku farka daga barcinku?
10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
rashi kuma kamar ɗan fashi.
 
12 Sakare da mutumin banza
wanda yana yawo da magana banza a baki,
13 wanda yake ƙyifce da ido,
yana yi alama da ƙafafunsa
yana kuma nuni da yatsotsinsa,
14 wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa,
kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye
15 Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya;
za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.
 
16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,
abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
17 duban reni,
harshe mai ƙarya,
hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,
ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,
da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
Gargaɗi a kan zina
20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;
ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;
sa’ad da kake barci, za su lura da kai;
sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,
wannan koyarwa haske ne,
kuma gyare-gyaren horo
hanyar rayuwa ce,
24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a
daga sulɓin harshen mace marar aminci.
 
25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka
kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
 
26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,
mazinaciya kuma takan farauci ranka.
27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa
ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi
ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;
babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
 
30 Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata
don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.
31 Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai
ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.
32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;
duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,
kuma kunyarsa za tă dawwama.
 
34 Gama kishi kan tā da hasalar miji,
kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
35 Ba zai karɓi duk wata biya ba;
zai ƙi cin hanci, kome yawansu.