15
1 Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi,
amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
2 Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani,
amma bakin wawa kan fitar da wauta.
3 Idanun Ubangiji suna a ko’ina,
suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.
4 Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai,
amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.
5 Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,
amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
6 Gidan adali yana da dukiya mai yawa,
amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.
7 Leɓunan masu hikima sukan baza sani;
ba haka zukatan wawaye suke ba.
8 Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye,
amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.
9 Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye
amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.
10 Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya;
wanda ya ƙi gyara zai mutu.
11 Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji,
balle fa zukatan mutane!
12 Mai yin ba’a yakan ƙi gyara;
ba zai nemi shawara mai hikima ba.
13 Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske,
amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
14 Zuciya mai la’akari kan nemi sani,
amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.
15 Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi,
amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.
16 Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji
da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
17 Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna
da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.
18 Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa,
amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.
19 An tare hanyar rago da ƙayayyuwa,
amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,
amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
21 Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki,
amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.
22 Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara,
amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
23 Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai,
kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!
24 Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima
don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari.
25 Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai
amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.
26 Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye,
amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.
27 Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa,
amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
28 Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta,
amma bakin mugu yakan fitar da mugunta.
29 Ubangiji yana nesa da mugaye
amma yakan ji addu’ar adalai.
30 Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya,
kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa.
31 Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa
ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.
32 Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan,
amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.
33 Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.