17
Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru
da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
 
Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya,
kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.
 
Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,
amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.
 
Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna;
maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.
 
Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne;
duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.
 
Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
 
Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,
ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!
 
Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi;
ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
 
Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,
amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
 
10 Tsawata kan sa mutum ya koyi basira
fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
 
11 Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah;
za a aika manzo mutuwa a kansu.
 
12 Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya
fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
 
13 In mutum ya sāka alheri da mugunta,
mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
 
14 Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne,
saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
 
15 Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci,
Ubangiji ya ƙi su biyu.
 
16 Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa,
da yake ba shi da sha’awar samun hikima?
 
17 Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,
ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
 
18 Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani
ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
 
19 Duk mai son faɗa yana son zunubi,
duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.
 
20 Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba;
duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.
 
21 Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki
babu farin ciki ga mahaifin wawa.
 
22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
 
23 Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce
don yă lalace yin adalci.
 
24 Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,
amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
 
25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa
da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
 
26 Ba shi da kyau a hukunta marar laifi,
ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.
 
27 Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi,
mutum mai basira kuma natsattse ne.
 
28 Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,
da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.