24
Faɗi 20
Kada ka yi ƙyashin mugaye,
kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
Faɗi 21
Ta wurin hikima ce ake gina gida,
kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
ta wurin sani ɗakunanta sukan cika
da kyawawan kayayyaki masu daraja.
Faɗi 22
Mutum mai hikima yana da iko sosai,
kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
don yin yaƙi kana bukatar bishewa,
kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
Faɗi 23
Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai
a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
Faɗi 24
Duk mai ƙulla mugunta
za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.
Makircin wawa zunubi ne,
mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
Faɗi 25
10 In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala,
ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!
11 Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su;
ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
12 In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,”
shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne?
Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne?
Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
Faɗi 26
13 Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau;
zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
14 Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai;
in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
Faɗi 27
15 Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali,
kada ka ƙwace masa wurin zama;
16 gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma,
amma bala’i kan kwantar da mugaye.
Faɗi 28
17 Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi;
sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,
18 in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba
ya kuma juye fushinsa daga gare shi.
Faɗi 29
19 Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta
ko ka yi ƙyashin mugaye,
20 gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba,
kuma fitilar mugaye za tă mutu.
Faɗi 30
21 Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana,
kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,
22 gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan,
kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?
Ƙarin maganganun hikima
23 Waɗannan ma maganganun masu hikima ne,
Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
24 Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”,
mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
25 Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi,
kuma babban albarka zai zo a kansu.
 
26 Amsa da take ta gaskiya
tana kamar sumba a leɓuna.
 
27 Ka gama aikinka
ka kuma shirya gonakinka;
bayan haka, ka gina gidanka.
 
28 Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba,
ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
29 Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini;
zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”
 
30 Na wuce cikin gonar rago,
na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,
ciyayi sun rufe ƙasar,
katangar duwatsu duk ta rushe.
32 Na yi tunani a zuciyata
na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
34 sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi
rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.