Zabura 53
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat.* Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Wani maskil Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. na Dawuda.
Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa,
“Ba Allah.”
Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau;
babu wani mai aikata abu mai kyau.
 
Allah yana duba daga sama
a kan ’ya’yan mutane
yă ga ko akwai wani wanda ya gane,
wani wanda yake neman Allah.
Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace;
babu guda da yake aikata abu mai kyau,
babu ko ɗaya.
 
Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo?
 
Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi,
ba sa kuma kira ga Allah.
Ga shi fa, sun firgita don tsoro,
ko da yake babu dalilin tsoro,
gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa,
za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su.
 
Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!
Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa,
bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

*^ Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.

^ Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce.