9
Zaɓen Allah mai iko duka
Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata, mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura. Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.
Zaɓin Allah mai iko duka
Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba. Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”* Far 18.10,14
10 Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11 Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, 12 ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” Far 25.23 13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.” Mal 1.2,3
14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15 Gama ya ce wa Musa,
“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,
zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.Ӥ Fit 33.19
16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”* Fit 9.16 18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” Ish 29.16; Ish 45.9 21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai? 25 Kamar yadda ya faɗa a Hosiya.
“Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba;
zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,” Hos 2.23
26 kuma,
“Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu,
‘Ku ba mutanena ba,’
za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”§ Hos 1.10
27 Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce,
“Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku,
ragowa ce kaɗai za su sami ceto.
28 Gama Ubangiji zai zartar da
hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”* Ish 10.22,23
29 Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa.
“Da ba don Ubangiji Maɗaukaki
ya bar mana zuriya ba,
da mun zama kamar Sodom,
da mun kuma zama kamar Gomorra.” Ish 1.9
Rashin bangaskiyar Isra’ila
30 Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya; 31 amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba. 32 Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.” 33 Kamar yadda yake a rubuce,
“Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe
da kuma dutsen da yake sa su fāɗi
wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.” Ish 8.14; Ish 28.16

*9:9 Far 18.10,14

9:12 Far 25.23

9:13 Mal 1.2,3

§9:15 Fit 33.19

*9:17 Fit 9.16

9:20 Ish 29.16; Ish 45.9

9:25 Hos 2.23

§9:26 Hos 1.10

*9:28 Ish 10.22,23

9:29 Ish 1.9

9:33 Ish 8.14; Ish 28.16