5
1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu, 2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin. 3 Amma Bitrus ya ce, ''Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin? 4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.” 5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu 6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi. 7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba. 8 Sai Bitrus ya ce mata, ''ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?'' Sai ta amsa, ''ta ce kaza ne.” 9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, ''Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu.'' 10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta. 11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura. 12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu, 13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a. 14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata, 15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu. 16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka. 17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka 18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku. 19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce, 20 “Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.” 21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin. 22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto, 23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba. 24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar. 25 Sai wani ya zo ya ce masu, ''Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.'' 26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu. 27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su, 28 cewa ''Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.” 29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, ''Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba. 30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace, 31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai. 32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.'' 33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin. 34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci. 35 Sai ya ce masu ''Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan, 36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu. 37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse. 38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace. 39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah.'' Sai suka rinjayu. 40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi. 41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan. 42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.