12
1 A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu. 2 Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi. 3 Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma. 4 Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa. 5 To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa. 6 Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun. 7 Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, “Tashi da sauri.” Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa. 8 Mala'ikan ya ce masa, “Yi damara ka sa takalmanka.” Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.” 9 Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne. 10 Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi. 11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, “Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato.” 12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a. 13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar. 14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa. 15 Suka ce mata, “Kin haukace.” Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, “Mala'ikansa ne.” 16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai. 17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, “Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru.” Sai ya bar su, ya tafi wani wuri. 18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus. 19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can. 20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne. 21 A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi. 22 Mutanen suka yi ihu, “Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!” 23 Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu. 24 Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya. 25 Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne. [Barnaba da Shawulu suka koma Urushalima.]