14
1 A lokacin da Bulus da Barnaba sun shiga garin Ikoniya suka shiga majami'an Yahudawa suka yi wa'azi yadda har mutane da yawa daga cikin Yahudawa da Hellinawa suka ba da gaskiya. 2 Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan. 3 Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba. 4 Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin. 5 Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su, 6 da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su, 7 a can suka yi wa'azin bishara. 8 A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa. 9 Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, “Tashi ka tsaya akan kafafunka” 10 Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo. 11 Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, “Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane.” 12 Suna kiran Barnaba da sunan “Zafsa,” Bulus kuwa suka kira shi da sunan “Hamisa” domin shine yafi yin magana. 13 Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya. 14 Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen. 15 Suna ta cewa, “Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu. 16 A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama. 17 Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki.” 18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya. 19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu. 20 Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba. 21 Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya. 22 Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, “Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala.” 23 Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi. 24 Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya. 25 Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya. 26 Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu. 27 Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya. 28 Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.