19
1 Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai. 2 Bulus ya ce masu, “Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?” Suka amsa, “A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba. 3 Bulus ya ce, “Wacce irin baftisma aka yi maku?” Suka ce, “Baftismar Yahaya” 4 Bulus ya amsa ya ce, “Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan.” 5 Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu. 6 Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci. 7 Su wajen mutum goma sha biyu ne. 8 Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah. 9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus. 10 Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa. 11 Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus, 12 har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus. 13 Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, “Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita.” 14 Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba. 15 Mugun ruhun ya amsa ya ce, “Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?” 16 Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka. 17 Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka. 18 Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata. 19 Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa. 20 Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa. 21 Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, “Bayan na je can, dole in je Roma.” 22 Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci. 23 A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar. 24 Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai. 25 Ya tattara makera ya ce da su, “Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa. 26 Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu. 27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada.” 28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa “Mai girma ce Dayana ta Afisa.” 29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya. 30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi. 31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin. 32 Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba. 33 Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a. 34 Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, “Mai girma ce Dayana ta Afisa.” 35 Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, “Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba? 36 Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce. 37 Gama kun kawo wadannan mutane a wannan dakin sharia ba a kan su mafasa ne na haikali ba ko kuma masu sabo ga allahnmu ba. 38 Saboda haka idan Damatrayas da makeran da ke tare da su na da wata tuhuma a kan wani, kotuna suna nan a bude masu shari'a kuma suna nan. Ba ri su kai karar junansu. 39 Amma idan akwai maganganu na dubawa, za a daidaita su a taronmu na lokaci lokaci. 40 Domin hakika muna cikin hatsarin zargi game da hargitsin yau. Babu dalilin wanan yamutsi domin ba mu da bayani a kansa.” 41 Da ya fadi haka, sai ya sallami taron.