10
1 Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da kazaman ruhohi, su warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya. 2 To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; 3 Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; 4 Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi. 5 Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, ''Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6 Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila. 7 Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta. 9 Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku. 10 Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa. 11 Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi. 12 In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku. 13 Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku. 14 Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku. 15 Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. 16 ''Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi. 17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu. 18 Za su kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku bada shaida a gabansu, da kuma gaban al'ummai. 19 Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin. 20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21 Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su. 22 Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira. 23 In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. 24 Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa. 25 Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! 26 Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28 Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama. 29 Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. 30 Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake. 31 Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa. 32 ''Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama. 33 Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama.'' 34 ''Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35 Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. 36 Zai zama na kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37 Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38 Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39 Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne. 40 ''Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan. 41 Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci. 42 Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba.''