7
Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji. Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif.
Sama’ila ya ci Filistiyawa da yaƙi a Mizfa
Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji. Saboda haka Sama’ila ya yi magana da dukan gidan Isra’ila ya ce, in har da zuciya ɗaya kuke juyowa ga Ubangiji sai ku raba kanku da baƙin alloli da gunkin nan Ashtarot, ku ba da kanku ga Ubangiji. Ku yi masa bauta shi kaɗai, zai kuɓutar da ku daga hannun Filistiyawa. Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.
Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.” Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.
Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa. Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.” Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.
10 Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa. 11 Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.
12 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.” 13 Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila. 14 Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa.
15 Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa. 16 Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a. 17 Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.