6
1 Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba. 2 Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. 3 Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.
4 Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, 5 waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, 6 ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a. 7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah. 8 Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.
9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. 11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.
Alkawarin Allah tabbatacce ne
13 Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa, 14 cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”* Far 22.17 15 Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.
16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama. 17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.