42
Bawan Ubangiji
“Ga bawana, wanda na ɗaukaka,
zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi;
Zan sa Ruhuna a cikinsa
zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
Ba zai yi ihu ko ya tā da murya,
ko ya daga muryarsa a tituna ba.
Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba,
ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba.
Cikin aminci zai kawo adalci;
ba zai kāsa ko ya karai ba
sai ya kafa adalci a duniya.
Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
 
Ga abin da Allah Ubangiji ya ce,
shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su,
wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta,
wanda ya ba wa mutanenta numfashi,
da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.
“Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;
zan riƙe hannunka.
Zan kiyaye ka in kuma sa ka
zama alkawari ga mutane
haske kuma ga Al’ummai,
don ka buɗe idanun makafi
ka ’yantar da kamammu daga kurkuku
kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.
 
“Ni ne Ubangiji; sunana ke nan!
Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.
Duba, abubuwan da sun tabbata,
sababbin abubuwa kuwa nake furtawa;
kafin ma su soma faruwa
na sanar da su gare ku.”
Waƙar yabo ga Ubangiji
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;
bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.
Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;
bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
12 Bari su ɗaukaka Ubangiji
su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
13  Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi,
kamar jarumi zai yi himma;
da ihu zai tā da kirarin yaƙi
zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.
 
14 “Na daɗe ina shiru,
na yi shiru na kuma ƙame kaina.
Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda,
na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.
15 Zan lalatar da duwatsu da tuddai
in busar da dukan itatuwansu;
zan mai da koguna su zama tsibirai
in kuma busar da tafkuna.
16 Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba,
a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su;
zan mai da duhu ya zama haske a gabansu
in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul.
Abubuwan da zan yi ke nan;
ba zan yashe su ba.
17 Amma waɗanda suka dogara ga gumaka,
waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’
za a mai da su baya da kunya.
Isra’ila makaho da kuma kurma
18 “Ka ji, kai kurma;
duba, kai makaho, ka kuma gani!
19 Wane ne makaho in ba bawana ba,
da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba?
Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni,
makaho kamar bawan Ubangiji?
20 Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba;
kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”
21 Yakan gamsar da Ubangiji
saboda adalcinsa
ya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.
22 Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima,
an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka
ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku.
Sun zama ganima,
babu wani da zai kuɓutar da su;
an mai da su ganima,
ba wanda zai ce, “Mayar da su.”
 
23 Wane ne a cikinku zai saurari wannan
ko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?
24 Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganima
Isra’ila kuma ga masu kwasar ganima?
Ba Ubangiji ba ne,
wanda kuka yi wa zunubi?
Gama ba su bi hanyoyinsa ba;
ba su yi biyayya da dokarsa ba.
25 Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa,
yaƙi mai tsanani.
Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba;
ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.