5
Kaciya a Gilgal
To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa.
A lokacin nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu ka yi wa Isra’ilawa kaciya.” Sai Yoshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa Isra’ilawa kaciya a Gibeyat-Ha’aralot.
Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne, dukan waɗanda suka fito daga Masar, dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja, sun mutu a cikin jeji a hanya bayan sun bar Masar. Dukan mutanen da suka fito daga Masar an yi musu kaciya, amma duk waɗanda aka haifa a jeji a tafiya daga Masar, ba a yi musu ba. Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka. Sai ya sa yaransu ne suka taso a maimakonsu, su ne waɗanda Yoshuwa ya yi wa kaciya. Sun kasance ba kaciya gama ba a yi musu ba a hanya. Kuma bayan da aka yi wa al’ummar kaciya dukansu, sai suka dakata a nan, sai da suka warke.
Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Yau na kawar muku da zargin Masar.” Saboda haka ake kiran sunan wurin Gilgal har wa yau.
10 Da yamman rana ta goma sha huɗu ga wata, lokacin da suke a Gilgal a filin Yeriko, Isra’ilawa suka yi Bikin Ƙetarewa. 11 A kashegarin Bikin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, burodi marar yisti da hatsin da aka gasa. 12 Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, Manna ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana.
Fāɗuwar Yeriko
13 To, da Yoshuwa ya yi kusa da Yeriko, ya tā da idanunsa ya duba, sai ya ga wani mutum tsaye a gabansa riƙe da takobi, sai Yoshuwa ya je wurinsa ya ce masa, “Kai namu ne ko na abokan gābanmu?”
14 Mutumin ya ce, “Babu ko ɗaya, na dai zo ne a matsayin shugaban rundunar sojojin Ubangiji.” Sai Yoshuwa ya kwanta da fuskarsa har ƙasa, ya girmama shi, ya ce masa, “Ranka yă daɗe, wane saƙo kake da shi domin bawanka?”
15 Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa.