10
Rana ta tsaya cik
1 Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya ji cewa Yoshuwa ya ci Ai da yaƙi ya kuma hallaka ta sarai, ya yi wa Ai da sarkinta abin da ya yi wa Yeriko da sarkinta, mutanen Gibeyon kuwa sun yi yarjejjeniya ta salama da Isra’ilawa, suna kuma zama kusa da su. 2 Shi da mutanensa suka ji tsoron wannan sosai, gama Gibeyon muhimmiyar birni ce, har ma kamar ɗaya daga cikin biranen sarauta, ya ma fi Ai girma, mazanta duka kuwa mayaƙa ne na ƙwarai. 3 Saboda haka sai Adoni-Zedek sarkin Urushalima ya roƙi Hoham sarkin Hebron, Firam sarkin Yarmut, Yafiya sarkin Lakish da Debir sarki Eglon ya ce, 4 “Ku zo ku taimake ni in kai wa Gibeyon hari. Domin sun yi yarjejjeniya ta salama da Yoshuwa da Isra’ilawa.”
5 Sai sarakunan nan biyar na Amoriyawa, sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon suka haɗa sojojinsu. Suka je dukansu suka yi shirin kai wa Gibeyon hari.
6 Sai mutanen Gibeyon suka aika zuwa wurin Yoshuwa a sansani a Gilgal, “Kada ka juya wa bayinka baya, ka zo da sauri ka cece mu! Ka taimake mu domin sarakunan Amoriyawa duka daga kan tudu sun haɗa ƙarfinsu tare za su tasar mana.”
7 Saboda haka Yoshuwa ya tashi da rundunarsa duka, tare da dukan jarumawansa. 8 Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.”
9 Bayan sun yi tafiya dukan dare daga Gilgal, Yoshuwa ya auko musu ba labari. 10 Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda. 11 Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.
12 A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa,
“Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon
Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”
13 Sai rana ta tsaya cik,
wata kuma ya tsaya,
har sai da al’ummar ta ɗauki fansa
a kan abokan gābanta,
kamar yadda aka rubuta a cikin littafin Yashar.
Rana ta tsaya a sararin sama, ba tă fāɗi ba har kusan yini guda. 14 Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.
15 Sai Yoshuwa ya koma sansanin Gilgal tare da dukan Isra’ilawa.
An kashe sarakunan Amoriyawa guda biyar
16 Sarakunan guda biyar suka gudu, suka ɓuya a cikin kogo a Makkeda. 17 Lokacin da aka gaya wa Yoshuwa cewa an sami sarakunan nan biyar a ɓoye a cikin kogo a Makkeda. 18 Sai ya ce, “Ku mirgina manyan duwatsu ku rufe bakin kogon, sai ku sa waɗannan mutane su yi tsaron kogon. 19 Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.”
20 Saboda haka Yoshuwa da Isra’ilawa suka hallaka su da yawa ƙwarai, amma ’yan kaɗan ɗin da suka rage suka tsere zuwa cikin biranensu masu kāriya. 21 Dukan rundunar kuma suka dawo sansanin Makkeda tare da Yoshuwa, ba abin da ya same su. Ba wanda ya sāke tsokanar Isra’ilawa.
22 Yoshuwa ya ce, “Ku buɗe bakin kogon ku kawo mini sarakunan nan guda biyar.” 23 Sai suka kawo sarakunan biyar daga cikin kogo; sarakunan Urushalima, Hebron, Yarmut, Lakish da Eglon. 24 Sa’ad da aka kawo sarakunan nan wurin Yoshuwa, ya kira dukan Isra’ilawa ya ce wa shugabannin rundunoni waɗanda suke tare da shi, “Ku zo nan ku taka wuyan sarakunan nan.” Sai suka zo suka taka wuyansu.
25 Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.” 26 Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma.
27 Da yamma Yoshuwa ya ba da umarni a sauko da su daga itatuwan a jefa su cikin kogon da suka ɓuya. Aka sa manyan duwatsu aka rufe bakin kogon, suna a can har wa yau.
28 A ranan nan Yoshuwa ya ci Makkeda da yaƙi. Ya karkashe mutanen tare da sarkinta. Bai bar wani da rai ba. Ya yi wa sarkin Makkeda yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
An ci biranen kudu da yaƙi
29 Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Makkeda zuwa Libna, suka kai mata hari. 30 Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.
31 Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Libna zuwa Lakish; suka yi shiri suka kai mata hari. 32 Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna. 33 Horam sarkin Gezer kuwa ya zo don yă taimaki Lakish, amma Yoshuwa ya haɗa duk da shi da rundunarsa ya ci su da yaƙi, har bai bar waninsu da rai ba.
34 Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari. 35 A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish.
36 Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can. 37 Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.
38 Yoshuwa da Isra’ilawa duka suka juya suka kai wa Debir hari, 39 suka hallaka birnin, da sarkinta da ƙauyukanta, suka karkashe dukan mazaunan wurin, ba su bar wani da rai ba. Suka yi wa Debir da sarkinta yadda suka yi wa Libna da sarkinta da kuma Hebron.
40 Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta. 41 Yoshuwa ya ci su da yaƙi daga Kadesh Barneya zuwa Gaza, da kuma daga dukan yankin Goshen zuwa Gibeyon. 42 Yoshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ne ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.
43 Yoshuwa kuwa ya dawo da dukan Isra’ilawa zuwa sansani a Gilgal.