3
* Wannan surar waƙa ce; ayoyin kowane sakin layi sun fara da harufan Ibraniyanci bi da bi, kuma ayoyin cikin kowane sakin layi ya fara da harufa iri ɗaya. 1 Ni ne mutumin da ya ga azaba
ta wurin bulalar fushin Ubangiji.
2 Ya kore ni, ya sa na yi tafiya
a cikin duhu maimakon a cikin haske;
3 ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni
sau da sau, dukan yini.
4 Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa
ya kuma karya ƙasusuwana.
5 Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni
da baƙin ciki da kuma wahala.
6 Ya sa na zauna a cikin duhu
kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
7 Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba;
Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
8 Ko lokacin da nake kira don neman taimako,
ba ya jin addu’ata.
9 Ya tare hanyata da tubula na duwatsu;
ya sa hanyata ta karkace.
10 Kamar beyar da take a laɓe tana jira,
kamar zaki a ɓoye,
11 ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni
ya bar ni ba taimako.
12 Ya ja kwarinsa
ya sa in zama abin baratarsa.
13 Ya harbi zuciyata
da kibiyoyin kwarinsa.
14 Na zama abin dariya ga mutanena duka;
suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
15 Ya cika ni da kayan ɗaci
ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
16 Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa;
ya tattake ni cikin ƙura.
17 An hana ni salama;
na manta da ko mene ne ake kira wadata.
18 Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare
da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
19 Na tuna da azabata da kuma sintiri,
da na yi ta yi da ɗacin rai.
20 Na tuna su sosai,
sai kuma na ji ba daɗi a raina.
21 Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
26 yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
27 Yana da kyau mutum yă sha wuya
tun yana yaro.
28 Bari yă zauna shiru shi kaɗai,
gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
29 Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura
kila akwai bege.
30 Bari yă ba da kumatunsa a mare shi,
yă kuma bari a ci masa mutunci.
31 Gama Ubangiji ba ya
yashe mutane har abada.
32 Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai,
ƙaunarsa tana da yawa.
33 Gama ba haka kawai yake kawo wahala
ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
34 Bai yarda a tattake
’yan kurkuku a ƙasa ba,
35 ko kuma a danne wa mutum hakkinsa
a gaban Maɗaukaki,
36 ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya
ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
37 Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika
in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne
bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
39 Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni
sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
40 Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta,
sai mu kuma koma ga Ubangiji.
41 Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu
ga Allah na cikin sama, mu ce,
42 “Mun yi zunubi mun yi tawaye
ba ka kuwa gafarta ba.
43 “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu;
ka karkashe mu ba tausayi.
44 Ka rufe kanka da gajimare
don kada addu’armu ta kai wurinka.
45 Ka mai da mu tarkace da juji
a cikin mutane.
46 “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana
marar daɗi.
47 Muna cika da tsoro,
da lalatarwa da hallakarwa.”
48 Hawaye na kwararowa daga idanuna
domin an hallaka mutanena.
49 Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye,
ba hutawa.
50 Har sai in Ubangiji ya duba
daga sama ya gani.
51 Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki
domin dukan matan birnina.
52 Maƙiyana suna farauta ta
ba dalili kamar tsuntsu.
53 Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami
suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
54 ruwaye suka rufe kaina,
sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
55 Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji,
daga rami mai zurfi.
56 Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka
ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
57 Ka zo kusa lokacin da na kira ka,
kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
58 Ya Ubangiji, ka goyi bayana;
ka fanshi raina.
59 Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba.
Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
60 Ka ga zurfin ramakonsu,
da duk mugun shirin da suke yi mini.
61 Ya Ubangiji, ka ji zaginsu,
da duka mugun shirin da suke yi mini
62 Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai
game da ni duk yini.
63 Dube su! A zaune ko a tsaye,
suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
64 Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji,
domin abin da hannuwansu suka yi.
65 Ka sa yana ta rufe zuciyarsu,
kuma bari la’anarka ta bi su.
66 Ka fafare su cikin fushi
ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.
*^ Wannan surar waƙa ce; ayoyin kowane sakin layi sun fara da harufan Ibraniyanci bi da bi, kuma ayoyin cikin kowane sakin layi ya fara da harufa iri ɗaya.