9
1 Ya kuma ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”
Sāke kamannin Yesu
(Mattiyu 17.1-13; Luka 9.28-36)
2 Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. 3 Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su. 4 Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.
5 Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” 6 (Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)
7 Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”
8 Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.
9 Da suna saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu. 10 Suka riƙe wannan zance a ɓoye tsakaninsu, suna tattaunawa ko mece ce ma’anar “tashi daga matattu.”
11 Suka tambaye shi, suka ce, “Don me malaman dokoki suke cewa, sai Iliya ya fara zuwa?”
12 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya ne, Iliya zai zo da fari, yă kuma mayar da dukan abubuwa. Don me kuma aka rubuta cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahala sosai, kuma a ƙi shi? 13 Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, kuma suka yi duk abin da suka ga dama da shi, kamar yadda aka rubuta game da shi.”
Warkar da yaro mai mugun ruhu
(Mattiyu 17.14-20; Luka 9.37-43)
14 Da suka dawo wurin sauran almajiran, sai suka ga babban taro kewaye da su, malaman dokoki suna gardama da su. 15 Nan take da dukan mutanen suka ga Yesu, sai suka cika da mamaki, suka ruga da gudu don su gai da shi.
16 Ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi da su?”
17 Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. 18 Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.”
19 Yesu ya ce, “Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”
20 Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.
21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, “Tun yaushe yake haka?”
Ya ce, “Tun yana ƙarami. 22 Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
23 Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
24 Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
25 Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, “Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”
26 Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” 27 Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
28 Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?”
29 Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a* Waɗansu rubuce-rubucen hannu suna da addu’a da azumikaɗai irin wannan yakan fita.”
30 Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba, 31 gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.” 32 Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
Wane ne mafi girma?
(Mattiyu 18.1-5; Luka 9.46-48)
33 Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?” 34 Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
35 Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
36 Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, 37 “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
Wanda ba ya gāba da mu, namu ne
(Luka 9.49,50)
38 Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yă daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”
39 Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yă faɗi wani abu mummuna game da ni. 40 Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. 41 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
Sanadin yin zunubi
(Mattiyu 18.6-9; Luka 17.1,2)
42 “Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku. 43 In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.† Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da fita, 44 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.” 45 In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.‡ Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da lahira, 46 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.” 47 In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, 48 inda
“ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,
wutar kuma ba a iya kashewa.’§ Ish 66.24
49 Za a tsarkake kowa da wuta.
50 “Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
*9:29 Waɗansu rubuce-rubucen hannu suna da addu’a da azumi
†9:43 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da fita, 44 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.”
‡9:45 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da lahira, 46 inda “tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.”
§9:48 Ish 66.24