19
Ruwan tsarkakewa
1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 2 “Wannan ita ce ƙa’ida wadda Ubangiji ya umarta. Faɗa wa Isra’ilawa su kawo maka jan karsana marar lahani, ko marar aibi wadda ba a taɓa sa ta tă yi noma ba. 3 Ka ba wa Eleyazar firist; a kuma kai ta bayan sansani, a yanka a gaban Eleyazar. 4 Sa’an nan Eleyazar firist zai ɗiba jininta a yatsarsa, yă yayyafa sau bakwai wajen gaban Tentin Sujada. 5 Sa’an nan a ƙone dukan karsanar, haɗe da fatarta, naman, jinin da kayan cikin, yayinda Eleyazar yake kallo. 6 Firist zai ɗauki itacen al’ul, da hizzob, da jan ulu, yă jefa su a kan karsanar da ake ƙonewa. 7 Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma. 8 Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.
9 “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi. 10 Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.
11 “Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai. 12 Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba. 13 Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.
14 “Ga ƙa’idar da za a bi in mutum ya mutu a cikin tenti. Duk wanda ya shiga tentin, kuma duk wanda yake cikinsa, za su zama da ƙazanta har kwana bakwai, 15 kuma kowane abin da ake zuba kaya, wanda ba shi da murfi a kansa, zai zama da ƙazanta.
16 “Wanda duk yake a fili, ya kuma taɓa gawa wanda aka kashe da takobi, ko wanda ya mutu mutuwar Allah, ko ƙashin mutum, ko kabari, zai ƙazantu har bakwai.
17 “Ga wanda ya ƙazantu kuwa, a ɗiba toka daga hadaya ta ƙonawa ta tsarkakewa, a zuba a cikin tulu, sa’an nan a zuba ruwa mai gudu a kansu. 18 Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah. 19 A rana ta uku, da ta bakwai kuma mai tsarkakewa zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, a rana ta bakwai kuma yă tsarkake shi. Wanda aka tsarkaken kuwa, dole yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka da yamma, zai kuma tsarkaka. 20 Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta. 21 Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla.
“Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma. 22 Duk abin da mai ƙazanta ya taɓa, ya ƙazantu, kowa kuma ya taɓa wannan abu, ya ƙazantu ke nan, har yamma.”