31
Ɗaukar Fansa a kan Midiyawa
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa, a kan Midiyawa. Bayan wannan za ka mutu, a kuwa tara ka ga mutanenka.”
Saboda haka Musa ya ce wa mutane, “Ku shirya waɗansu daga cikin mazanku, su tafi su yi yaƙi da Midiyawa don su ɗaukar wa Ubangiji fansa a kansu.” Ku aiki maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila. Saboda haka aka samo mayaƙa dubu goma sha biyu shiryayyu don yaƙi, maza dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila. Musa ya aike su zuwa yaƙi, dubu ɗaya daga kowace kabila, tare da Finehas ɗan Eleyazar, firist, wanda ya ɗauki kayayyaki daga wuri mai tsarki da ƙahoni don kiran yaƙi.
Suka yi yaƙi da Midiyawa, suka kashe kowane mutum yadda Ubangiji ya umarci Musa. A cikin waɗanda aka kashe kuwa akwai Ewi, Rekem, Zur, Hur da Reba; sarakuna biyar na Mediyawa. Suka kuma kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi. Isra’ilawa suka kwashe mata da yaran Midiyawa, a matsayin bayi. Suka kwashe shanunsu da tumakinsu da kuma dukan dukiyarsu, a matsayin ganima. 10 Suka ƙone dukan garuruwan da Midiyawa suke zama, da dukan sansaninsu. 11 Suka kwashe dukan ganima haɗe da mutane da dabbobi, 12 suka kawo bayi da ganiman nan, wurin Musa da Eleyazar firist, da kuma jama’ar Isra’ilawa, a sansaninsu a filayen Mowab kusa da Urdun daga ƙetaren Yeriko.
13 Musa, da Eleyazar firist da dukan shugabannin jama’a, suka fito suka tarye su a bayan sansani. 14 Musa kuwa ya husata da shugabannin sojojin da suke shugabannin dubbai da shugabannin ɗari-ɗarin da suka dawo daga yaƙi.
15 Ya tambaye su ya ce, “Kun bar dukan mata da rai? 16 Su ne waɗanda suka bi shawarar Bala’am suka kuma zama sanadin sa Isra’ilawa suka juya wa Ubangiji baya, har ya kawo abin da ya faru da Feyor, har annoba ya kashe dukan mutanen Ubangiji. 17 Yanzu ku kashe dukan yara maza, ku kuma kashe kowace macen da ta yi lalata da namiji, 18 amma ku bar kowace yarinyar da ba tă taɓa yin lalata da namiji ba.
19 “Dukanku da kuka kashe mutum, ko kuka taɓa wani da aka kashe, dole ku kasance a bayan sansani har kwana bakwai. A rana ta uku da rana ta bakwai dole ku tsabtacce kanku da kuma bayinku. 20 Ku tsarkake kowace taguwa da kuma kome da aka yi da fata, da gashin akuya, ko kuwa itace.”
21 Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa. 22 Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma 23 da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa. 24 A rana ta bakwai za ku wanke tufafinku, sa’an nan za ku tsarkaka, bayan haka ku shigo sansani.”
Rabawa ganima
25  Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce, 26 “Da kai da Eleyazar firist, da shugabannin jama’a, ku ƙidaya dukan mutane da dabbobin da aka ci da yaƙi. 27 Ku kasa ganimar kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗaya kuma ku ba wa jama’a. 28 Daga sojojin da suka je yaƙin kuwa, ka ware ganima wa Ubangiji, ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar. 29 Ka ɗauki wannan sashe daga rabin rabonsu ka ba wa Eleyazar firist, a matsayin sashe na Ubangiji. 30 Daga cikin rabin rabon Isra’ilawa, ka zaɓi ɗaya daga kowane hamsin na mutane, shanu, jakuna, tumaki, awaki ko kuma sauran dabbobi. Ka ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.” 31 Saboda haka Musa da Eleyazar suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
32 Yawan ganimar da sojoji suka kawo ita ce tumaki 675,000 33 shanu 72,000 34 da jakuna 61,000. 35 Akwai kuma mata 32,000 da ba su yi lalata ba da namiji ba.
 
36 Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi shi ne,
 
tumaki 337,500, 37 tumakin da aka ware wa Ubangiji kuwa 657 ne;
38 shanu 36,000, shanun da aka ware wa Ubangiji kuwa 72 ne;
39 jakuna 30,500, jakunan da aka ware wa Ubangiji kuwa 61 ne;
40 mutane 16,000, mutanen da aka ware wa Ubangiji kuwa 32 ne.
 
41 Musa ya ba wa Eleyazar abin da aka ware wa Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
42 Kashin da aka ba wa Isra’ilawa, wanda Musa ya ware daga cikin na waɗanda suka tafi yaƙi, 43 kashin da aka ba wa jama’a kuwa tumaki 337,500 ne, 44 shanu 36,000, 45 jakuna 30,500 46 da mutane 16,000. 47 Daga rabin kashi na Isra’ilawa, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na mutane da na dabbobi, yadda Ubangiji ya umarce shi, ya ba wa Lawiyawan da suke lura da tabanakul na Ubangiji.
48 Sai shugabannin da suka shugabancin rundunar yaƙin, shugabanni na dubu-dubu da shugabanni na ɗari-ɗari, suka zo wurin Musa 49 suka ce masa, “Barorinka sun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashinmu, babu ko ɗayan ya ɓace. 50 Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
51 Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka daga gare su. 52 Dukan zinariya da shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, waɗanda Musa da Eleyazar suka karɓa, suka kuma miƙa hadaya ga Ubangiji, nauyinta ta kai shekel 16,750. 53 Kowane soja, ya kwashi ganima wa kansa. 54 Musa da Eleyazar firist, suka karɓi zinariya daga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, suka kawo cikin Tentin Sujada, don su zama abin tuni ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji.