34
Iyakokin Kan’ana
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.
3 “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,* Wato, Mataccen Teku; haka ma a aya 12. 4 tă ƙetare Mashigin Kunama† Da Ibraniyanci Akrabbim a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon, 5 inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.‡ Wato, Mediterraniyan; haka kuma a ayoyi 6 da 7.
6 “ ‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.
7 “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor, 8 za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo§ Ko Kuwa zuwa mashigin Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad, 9 tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.
10 “ ‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam. 11 Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.* Wato, Galili 12 Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri.
“ ‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’ ”
13 Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi, 14 saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu. 15 Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko† Urdun na Yeriko mai yiwuwa tsohuwar suna ce ta Kogin Urdun. wajen fitowar rana.”
16 Ubangiji ya ce wa Musa, 17 “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun. 18 Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.
19 “Ga sunayensu.
“Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
20 Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon
21 Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;
22 Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;
23 Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;
24 Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;
25 Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;
26 Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;
27 Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
28 Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”
29 Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.