Zabura 57
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam.* Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.
1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,
gama a gare ka raina yake samun mafaka.
Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka
sai masifar ta wuce.
2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka,
ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni,
yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi;
Sela
Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
4 Ina tsakiyar zakoki;
ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane,
mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi,
waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna,
damuwa ta sha ƙarfina.
Sun haƙa rami a hanyata,
amma su kansu suka fāɗa a cikinta.
Sela
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,
zuciyata tana nan daram;
zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
8 Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;
amincinka na kaiwa sarari.
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;
bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.