Zabura 63
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda.
1 Ya Allah, kai ne Allahna,
da nacewa na neme ka;
raina yana ƙishinka,
jikina yana marmarinka,
cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye
inda babu ruwa.
2 Na gan ka a wuri mai tsarki
na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
4 Zan yabe ka muddin raina,
kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;
da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
6 A gadona na tuna da kai;
ina tunaninka dukan dare.
7 Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
8 Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
9 Su da suke neman raina za su hallaka;
za su gangara zuwa zurfafan duniya.
10 Za a bayar da su ga takobi
su kuma zama abincin karnukan jeji.
11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;
dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,
amma za a rufe bakunan maƙaryata.