Zabura 79
Zabura ta Asaf.
1 Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka;
sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki,
sun bar Urushalima kufai.
2 Sun ba da gawawwakin bayinka
kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama,
nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
3 Sun zubar da jini kamar ruwa
ko’ina a Urushalima,
kuma babu wani da zai binne matattu.
4 Mun zama abin reni ga maƙwabta,
abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
5 Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne?
Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
6 Ka zuba fushinka a kan al’umman
da ba su yarda da kai ba,
a kan mulkokin
da ba sa kira bisa sunanka;
7 gama sun cinye Yaƙub
suka lalatar da ƙasar zamansa.
8 Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu;
bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu,
gama mun fid da zuciya sarai.
9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,
saboda ɗaukakar sunanka;
ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu
saboda sunanka.
10 Don me al’ummai za su ce,
“Ina Allahnsu yake?”
A idanunmu, ka sanar wa al’ummai
cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
11 Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka;
ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
12 Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai
zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
13 Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,
za mu yabe ka har abada;
daga tsara zuwa tsara
za mu yi ta ba da labarin yabonka.