Zabura 111
Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata
a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
2 Ayyukan Ubangiji da girma suke;
dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne,
adalcinsa kuma zai dawwama har abada.
4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;
Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa;
yakan tuna da alkawarinsa har abada.
6 Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa,
yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
7 Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya;
dukan farillansa abin dogara ne.
8 Tsayayyu ne har abada abadin,
ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.
9 Yana ba da ceto ga mutanensa;
ya kafa alkawarinsa har abada,
tsarki da banrazana ne sunansa.
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
*^ Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
†Zabura 111:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya