7
1 Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne,
Ya diyar sarki!
Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja,
aikin hannun gwanin sassaƙa.
2 Cibinki kamar kwaf ne
da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba.
Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama
wanda furen bi-rana ya kewaye.
3 Nonanki sun yi kamar bareyi biyu,
tagwayen barewa.
4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa.
Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon
kusa da ƙofar Bat Rabbim.
Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon
wadda take duban Damaskus.
5 Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel.
Gashinki ya yi kamar shunayya;
yakan ɗauke hankalin sarki.
6 Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi,
Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
7 Tsayinki ya yi kamar itacen dabino,
kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.
8 Na ce, “Zan hau itacen dabino;
zan kama ’ya’yansa.”
Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa,
ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau.
Ƙaunatacciya
Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena,
yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
10 Ni ta ƙaunataccena ce,
kuma sha’awarsa domina ne.
11 Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari,
bari mu kwana a ƙauye.
12 Bari mu tafi gonar inabi da sassafe
don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya,
ko furanninsu sun buɗe,
ko rumman sun yi fure,
a can zan nuna maka ƙaunata.
13 Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu,
a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi,
sabo da tsoho,
da na ajiye dominka, ƙaunataccena.