9
Hukunci a kan abokan gāban Isra’ila
1 Annabci.
Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrak
za tă kuma sauko a kan Damaskus,
gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila
suna a kan Ubangiji* Ko kuwa Damaskus. Gama idon Ubangiji yana a kan dukan mutane, haka ma a kan kabilan Isra’ila,,
2 da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita,
da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
3 Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi;
ta tara azurfa kamar ƙasa,
zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
4 Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta,
zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku,
wuta kuma za tă cinye ta.
5 Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro;
Gaza za tă yi birgima cikin azaba,
haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya.
Gaza za tă rasa sarkinta
za a kuma gudu a bar Ashkelon.
6 Baƙi za su mallaki Ashdod,
kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
7 Zan kawar da jini daga bakinsu,
zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu.
Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu,
su kuma zama shugabanni a Yahuda,
Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
8 Amma zan kāre gidana
daga sojoji masu kai da kawowa.
Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba,
gama yanzu ina tsaro.
Zuwan sarkin Sihiyona
9 Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima!
Ki yi sowa, Diyar Urushalima!
Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki,
mai adalci yana kuma da ceto,
mai tawali’u yana kuma hawan jaki,
yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.
10 Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim,
da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima,
za a kuma karya bakan yaƙi.
Zai yi shelar salama ga al’ummai.
Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku,
daga Kogi† Wato, Yuferites kuma zuwa ƙarshen duniya.‡ Ko kuwa ƙarshen ƙasa
11 Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke,
zan ’yantar da ’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.
12 Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya;
ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.
13 Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana,
in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya.
Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona,
gāba da ’ya’yanki, ya Girka,
in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
Ubangiji zai bayyana
14 Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu;
kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya.
Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho;
zai taho ta cikin guguwa daga kudu,
15 Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su.
Za su hallakar
su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa.
Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi;
za su cika kamar kwanon
da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
16 Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana
gama su mutanensa ne da kuma garkensa.
Za su haska a cikin ƙasarsa
kamar lu’ulu’u a rawani.
17 Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa!
Hatsi zai sa samari su yi murna,
sabon ruwan inabi kuma zai sa ’yan mata su yi farin ciki.