Zefaniya
1
1 Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.
Gargaɗi a kan hallaka mai zuwa
2 “Zan hallaka kome
a fuskar duniya,”
in ji Ubangiji.
3 “Zan hallaka mutane da dabbobi;
zan kuma hallaka tsuntsayen sama
da kifayen teku,
da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.”* Ma’anar Ibraniyancin nan babu tabbas.
“Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,”
in ji Ubangiji.
4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda
da kuma dukan mazaunan Urushalima.
Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri,
da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,
5 waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki
don su yi sujada ga rundunar taurari.
Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji
suke kuma rantsuwa da sunan Molek.† Da Ibraniyanci Malkam, wato, Milkom.
6 Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji,
ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”
7 Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka,
gama ranar Ubangiji ta yi kusa.
Ubangiji ya shirya hadaya;
ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.
8 “A ranar hadayar Ubangiji
zan hukunta sarakuna
da kuma ’ya’yan sarakuna
da duk waɗanda suke sanye
da rigunan ƙasashen waje.
9 A wannan rana zan hukunta
dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa,‡ Dubi 1Sam 5.5.
waɗanda suke cika haikalin allolinsu
da rikici da ruɗu.
10 “A wannan rana,”
in ji Ubangiji,
“Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi,
kururuwa daga Sabon Mazauni,
da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.
11 Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa;§ Ko kuwa Turmi
za a hallaka dukan ’yan kasuwanku,
dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.
12 A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu
in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba,
waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya,
waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome ba
nagari ko mummuna.’
13 Za a washe dukiyarsu,
a rurrushe gidajensu.
Za su gina gidaje
amma ba za su zauna a ciki ba;
za su shuka inabi
amma ba za su sha ruwansa ba.”
14 Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa,
ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri.
Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi,
za a ji kururuwan jarumi a can.
15 Ranan nan za tă zama ranar fushi,
rana ce ta baƙin ciki da azaba,
rana ce ta tashin hankali da lalacewa,
ranar duhu baƙi ƙirin,
ranar gizagizai da baƙin duhu,
16 rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi
gāba da birane masu mafaka,
da kuma kusurwar hasumiyoyi.
17 “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane
za su kuma yi tafiya kamar makafi,
domin sun yi wa Ubangiji zunubi.
Za a zubar da jininsu kamar ƙura
kayan cikinsu kuma kamar najasa.
18 Azurfarsu ko zinariyarsu
ba za su iya cetonsu ba
a ranar fushin Ubangiji.”
A cikin zafin kishinsa
za a hallaka dukan duniya
gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya
nan da nan.