8
1 Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, “Dukanmu muna da ilimi.” Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa. 2 Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba. 3 Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum. 4 Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, “Gunki a duniyan nan ba wani abu bane,” kuma cewa” Babu wani Allah sai guda daya.” 5 To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu “alloli dabam dabam a duniya ko a sama,” kamar yadda akwai “alloli da iyayengiji” da yawa. 6 “Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke.” 7 Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni. 8 Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba. 9 Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya. 10 Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba? 11 Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka. 12 Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu. 13 Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa.