7
1 Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku. 2 Mudun da kukan auna, da shi za a auna maku. 3 Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? 4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? 5 Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka. 6 Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku. 7 Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku. 8 Ai duk wanda ya roka, zai karba, kuma duk wanda ya nema zai samu, wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa. 9 Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji? 11 Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? 12 Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa. 13 Ku shiga ta matsattsiyar kofa, don kofar zuwa hallaka na da fadi, hanyar ta mai saukin bi ce, masu shiga ta cikin ta suna da yawa. 14 Domin kofar zuwa rai matsattsiya ce, hanyar ta mai wuyar bi ce, masu samun ta kuwa kadan ne. 15 Ku kula da annabawan karya, wadanda su kan zo maku da siffar tumaki, amma a gaskiya kyarketai ne masu warwashewa. 16 Za ku gane su ta irin ''ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? 17 Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. 18 Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba. 19 Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20 Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su. 21 Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama. 22 A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' 23 Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' 24 Saboda haka, dukan wanda yake jin maganata, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidan sa a bisa dutse. 25 Da ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fadi ba, domin an gina shi bisa dutse. 26 Amma duk wanda ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutum da ya gina gidansa a kan rairayi. 27 Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa.'' 28 Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29 Domin yana koya masu da iko, ba kamar marubuta ba.