5
1 Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa. 2 Sa'adda Yesu ya sauko daga cikin jirgin ruwan sai wani mutum mai aljanu ya fito daga cikin kaburbura ya tarbe shi. 3 Mutumin yana zama a cikin kaburbura. An daure shi da sarkoki da mari 4 An daure shi da sarkoki da mari sau da yawa, amma ya tsuntsunke sarkoki da marin. har ma ba wanda zai iya daure shi kuma. 5 Dare da rana a cikin kabarbarun da duwatsu mutumin ya na ihu ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi. 6 Sa'adda ya hango Yesu daga nesa, sai ya tarbi Yesu ya durkusa a gabansa. 7 Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala, 8 Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa.” 9 Ya tambaye shi, “Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa. 10 Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar. 11 Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni. 12 Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun. 13 Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa. 14 Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru 15 Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata. 16 Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun. 17 Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu. 18 Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi. 19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka. 20 Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki. 21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun. 22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa. 23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, “Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu.” 24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi. 25 Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu. 26 Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi. 27 Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa. 28 Domin ta ce “Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke.” 29 Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta. 30 Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce “wanene ya taba rigata?” 31 Almajiransa suka ce, “ a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?” 32 Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi. 33 Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya. 34 Sai ya ce da ita, “Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki”. 35 Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce “Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?” 36 Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, “kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai.” 37 Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu. 38 Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai. 39 Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane “Me ya sa kuke damuwa da kuka?” Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi. 40 Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke. 41 Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita “Tilatha koum” wato yarinya na ce ki tashi” 42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya [gama shekarun ta sun kai goma sha biyu]. Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske. 43 Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.