9
Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.” Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu. Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya. Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu. Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya, Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.) Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, “ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi. Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu. 10 Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu “mene ne tashin matattu” ke nufi. 11 Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?” 12 Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi? 13 Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa.” 14 Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura. 15 Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16 Ya tambayi almajiransa, “ Wacce muhawara ce kuke yi da su?” 17 Daya daga cikin taron ya amsa masa”malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani. 18 Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa. 19 Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi. 20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. 22 Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu. 23 Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata. 24 Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. 25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, “kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa. 26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, “Ai, yaron ya mutu. 27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye. 28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?” 29 Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.” 30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. 31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi. 32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? 34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma. 35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka. 36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu. 37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.” 38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu. 39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu. 40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne. 41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba. 42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku. 43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. 44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. 46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. 48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa. 49 Domin da wuta za a tsarkake kowa. 50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.