13
1 da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa “malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!” 2 Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba.” 3 Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce. 4 Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?'' 5 Yesu ya ce masu, “ku kula, kada kowa ya rudeku. 6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa. 7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. 8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne. 9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su. 10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara. 11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne. 12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su. 13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu. 14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse. 15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu. 16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa. 17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin. 18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina. 19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada. 20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin. 21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. 22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki. 23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin. 24 Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba. 25 Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 26 Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka. 27 Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama. 28 “Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan. 29 Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke. 30 Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 31 Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 32 Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai. 33 Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba. 34 Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake. 35 To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne. 36 Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci. 37 Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!”