5
Sa'annan na ga a cikin hannun daman wanda ke zaune a kan kursiyin, na ga littafi wanda ke da rubutu ciki da waje, an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. Na kuma ga wani kakkarfan mala'ika na shela da murya mai karfi, “Wa ya isa ya bude littafin ya kuma bambare hatimin?” Ba wani a sama ko a kasa ko karkashin kasa da ya iya ya bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. Na yi kuka mai zafi saboda ba wani da ya cancanta da zai bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. Amma daya daga cikin dattawan nan ya ce mani, “Kada ka yi kuka. Duba! Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda, ya yi nasara. Ya cancanci bude littafin da kuma hatimansa bakwai.” Na ga Dan Rago yana tsaye tsakanin kursiyin da rayayyun halittun nan guda hudu a cikin dattawa. Yana kama da wanda aka kashe. Yana da kafonni bakwai da idanuwa bakwai; wadannan sune ruhohin Allah bakwai da aka aiko zuwa dukan duniya. Ya tafi ya karbi littafin daga hannun daman wanda ke zaune bisa kursiyin. Lokacin da Dan Ragon ya dauki littafin, rayayyun halittun nan hudu da dattawan nan ashirin da hudu suka fadi har kasa a gaban Dan ragon. Kowannen su na dauke da molo da tasar zinariya cike da kayan kamshi, wadanda kuwa sune addu'o'in masu ba da gaskiya. Suka raira sabuwar waka: “Ka cancanta ka dauki littafinka kuma bude hatimansa. Domin an yanka ka, da jininka ka saya wa Allah mutane daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma. 10 Ka maishe su mulki da firistoci su bauta wa Allanmu, kuma za su yi mulki a duniya.” 11 Da na duba sai na ji karar mala'iku masu yawa kewaye da kursiyin da rayayyun halitu da kuma dattawa. Jimillarsu ya kai dubbai goma, sau dubbai goma, da dubun dubbai. 12 Suka tada murya da karfi suka ce, “Macancanci ne Dan Ragon da aka yanka ya karbi iko, wadata, hikima, karfi, girma, daukaka da yabo.” 13 Na ji kowanne halittaccen abu da ke cikin sama da kasa da karkashin kasa da cikin teku - dukan abubuwan da ke cikinsu - na cewa, “Ga shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Dan Ragon, yabo, girma, daraja, da kuma ikon yin mulki, har abada abadin. 14 Sai rayayyun halittun nan hudu suka ce, “Amin!” dattawan nan kuma suka fadi da fuskokinsu suka yi sujada.