8
1 Lokacin da Dan Ragon nan ya bude hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kimanin rabin sa'a. 2 Sa'anan na ga mala'iku bakwai wadanda ke tsaye a gaban Allah, aka kuma basu kahonni bakwai 3 Wani mala'ika ya zo, rike da tasar turaren konawa na zinariya, a tsaye gaban bagadi. Turaren konawa mai yawa aka bashi saboda ya mika su tare da adu'o'in dukan masu bada gaskiya akan bagadin kona turare na zinariya a gaban kursiyin. 4 Hayakin turaren konawa, da adu'o'in masu bada gaskiya, suka tashi sama a gaban Allah daga hanun mala'ikar. 5 Mala'ikan ya dauki tasar turaren konawa ya cika ta da wuta daga bagadin. Sa'annan ya wurgo ta kasa zuwa duniya, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa. 6 Mala'ikun nan bakwai wadanda suke da kahonni bakwai suka yi shirin busa su. 7 Mala'ika na fari ya hura kahonsa, sai ga kankara da wuta a garwaye da jini. Aka jeho shi kasa zuwa duniya sai kashi daya cikin uku na duniya ya kone, daya cikin uku na itatuwa suka kone, da duk danyar ciyawa suka kone kaf. 8 Mala'ika na biyu ya busa kahonsa, sai wani abu mai kama da babban dutse mai cin wuta aka jefo shi cikin teku. Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini, 9 daya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka. 10 Mala'ika na uku ya busa kahonsa, sai gagarumin tauraro ya fado daga sama, yana ci kamar cocila, bisa kashi daya cikin uku na koguna da mabulbulan ruwa. 11 Sunan tauraron Daci. Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu domin ruwayen sun yi daci. 12 Mala'ika na hudu ya busa kahonsa, sai daya cikin kashi uku na rana ya harbu, da daya cikin kashi uku na wata da kuma daya cikin kashi uku na taurari. Sai daya cikin kashi uku nasu duka suka duhunce; daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su. 13 Da na duba sai na ji gaggafa da take shawagi a tsakiyar sararin sama tana kira da babban murya, “Kaito, kaito, kaito, ga mazaunan duniya sabili da sauran karar kahonni na mala'ikun nan uku da za su busa.”