15
1 Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala'iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika. 2 Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su. 3 Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: ''Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al'ummai. 4 Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al'ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci.” 5 Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama. 6 Daga wuri mafi tsarki mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu. 7 Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala'iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin. 8 Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala'ikun nan bakwai suka cika.