2
1 Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa. 2 Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa. 3 Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah? 4 Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane? 5 Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah. 6 Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa: 7 Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. 8 Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu. 9 Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa. 10 Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa. 11 Domin kuwa Allah ba mai tara bane. 12 Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a. 13 Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata. 14 Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar. 15 Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu. 16 hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu. 17 Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah, 18 ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar. 19 Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu, 20 mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya. 21 ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata? 22 Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali? 23 ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a? 24 ''Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku,'' kamar yadda aka riga aka rubuta. 25 Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya. 26 domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba? 27 Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka! 28 Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba. 29 Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.