8
1 Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu. 2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa. 3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki. 4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya. 5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu. 6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama. 7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya. 8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya. 9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane. 10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci. 11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku. 12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki. 13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu. 14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne. 15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, “Abba, Uba!” 16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne. 17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi. 18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba. 19 Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah. 20 Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin. 21 Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah. 22 Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu. 23 Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu—mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan. 24 Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani? 25 Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri. 26 Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa. 27 Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah. 28 Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri. 29 Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa. 30 Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka. 31 Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu? 32 Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi? 33 Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke “yantarwa. 34 Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu. 35 Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi? 36 Kamar yadda aka rubuta, “Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka.” 37 A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu. 38 Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko, 39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.