15
Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba. Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi. Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, “zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina.” Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi. Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu. Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya. Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah. Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu. Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.” 10 Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.” 11 Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.” 12 Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.” 13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. 14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna. 15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah. 16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17 Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah. 18 Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki. 19 Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka. 20 A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani. 21 Kamar yadda yake a rubuce.”Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta.” 22 Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama. 23 Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku. 24 Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci. 25 Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima. 26 Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima. 27 Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa. 28 Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya. 29 Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu. 30 Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni. 31 Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya. 32 Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu. 33 Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.