Nehemiya. 7. Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa. Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane. Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.” Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna. Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki. Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa. Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana). Ga jerin mutanen Isra’ila. Zuriyar Farosh mutum 2,172 ta Shefatiya 372 ta Ara 652 ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818 ta Elam 1,254 ta Zattu 845 ta Zakkai 760 ta Binnuyi 648 ta Bebai 628 ta Azgad 2,322 ta Adonikam 667 ta Bigwai 2,067 ta Adin 655 ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98 ta Hashum 328 ta Bezai 324 ta Harif 112 ta Gibeyon 95. Mutanen Betlehem da na Netofa 188 na Anatot 128 na Bet-Azmawet 42 na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743 na Rama da na Geba 621 na Mikmash 122 na Betel da na Ai 123 na ɗayan Nebo 52 na ɗayan Elam 1,254 na Harim 2 320 na Yeriko 345 na Lod, da na Hadid, da na Ono 721 na Sena’a 3,930. Ga zuriyar Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 ta Immer 1,052 ta Fashhur 1,247 ta Harim 1,017. Ga zuriyar Lawiyawa. Zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodeba) 74. Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148. Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita da Shobai 138. Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon, da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai, da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar, da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda, da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya, da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa, da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur, da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha, da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema, da ta Neziya, da kuma ta Hatifa. Ga zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, da ta Soferet, da ta Ferida, da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel, Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Amon. Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392. Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba, zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 642. Na wajen firistoci kuwa su ne, Zuriyar Hobahiya, da ta Hakkoz, da ta Barzillai (wani mutumin da ya auri ’yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kuma kira shi da wannan suna). Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki. Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim. Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245. Akwai dawakai 736, alfadarai 245 raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720. Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci. Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki. Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci. Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu. Da wata na bakwai ya zo, Isra’ilawa kuwa sun riga sun zauna a garuruwansu,