Zabura. 63. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.