Zabura. 87. Na ’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Waƙa ce. Ya kafa harsashinsa a kan dutse mai tsarki. Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub. Ana faɗin abubuwa masu ɗaukaka game da ke Ya birnin Allah, Sela “Zan lissafta Rahab a cikin waɗanda suka san ni, Filistiya ita ma, da Taya, tare da Kush, zan kuma ce, ‘An haifi wannan a Sihiyona.’ ” Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.” Ubangiji zai rubuta a littafin sunayen mutanensa, “An haifi wannan a Sihiyona.” Sela Yayinda suke kaɗe-kaɗe za su rera, “Dukan maɓulɓulaina suna cikinki.”