Zabura. 102. Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta. Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai. Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai. Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki. Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana. Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe. Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai. Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo. Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi. Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa. Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, “Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada. Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina. Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba. ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”