Zabura. 117. Yabi Ubangiji, dukanku al’umma; ku ɗaukaka shi, dukanku mutane. Gama ƙaunarsa da girma take gare mu, amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada. Yabi Ubangiji.