Zabura. 124. Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce, da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana, sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai; da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu. Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba. Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira. Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.