Zabura. 134. Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji. Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.